Kungiyar G20 na wani taro a Korea ta Kudu

Image caption Shugabannin kasashen G20

Ministocin kudi na kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki a duniya wato G20 sun fara wani taron kwanaki biyu a kasar Korea ta Kudu.

Wannan taron dai sharar fage ne a gabannin babban taron da zasu yi a wata mai kamawa.

Daga cikin abubuwan da wannan taro zai fi baiwa muhimmanci shine batun yakin takardar kudi.

Kungiyar G20 din dai na neman masalaha ne daga kangin matsalar kudade da ake fama da ita.

Daga cikin manyan kalubalen da ta ke fuskanta dai shi ne na cimma matsaya guda dangane da matsalar dake addabar kasuwannin kudade.

Da dama daga cikin kasashen da ke tasowa na nuna damuwarsu akan matsin lambar da suke fuskanta game da darajar kudadensu, wanda ka iya sanyawa harkarsu ta fita da kaya waje domin sayarwa ta ja baya.

Baya ga haka, akwai matsalar karancin kudin ruwa a kasashen da ke da arziki, wanda hakan ke sanyawa masu jari guduwa zuwa kasashen da ke tasowa, domin fadada kasuwancinsu.

Kuma alamu na nuni da cewa kudaden ruwan ba zasu karu anan kusa ba, kamar yanda su masu jarin ke son ganin an samu.