Mai yiwuwa a sake jinkirta zaben Guinea

Al'ummar Guinea na kada kuri'a
Image caption Al'ummar Guinea na kada kuri'a a zagaye na farko na zaben

Sabon shugaban hukumar zaben kasar Guinea, Siaka Toumani Sangare, ya ce a yau ne za a yanke hukunci a kan ko za a sake jinkirta zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

Ranar Lahadin nan mai zuwa ne dai ya kamata a gudanar da zaben.

Yayin da yake magana a karo na farko tun bayan nada shi ranar Talata, shugaban hukumar zaben ya sha alwashin tabbatar da cewa an yi zabe na gaskiya da adalci a kasar.

Shi dai Siaka Toumani Sangare, an nada shi ya shugabanci hukumar zaben kasar ne bayan tashe-tashen hankulan da aka yi a kasar ta Guinea.