Fiye da mutane 130 sun rasu a Haiti

cholera
Image caption Masu fama da kwalara a Haiti

Jami'an lafiya a Haiti sun bayyana cewa fiye da mutane dari da talatin ne suka rasu a sanadiyyar cutar amai da gudawa wato Cholera a yankin dake arewa da birnin Port au Prince.

Kimanin mutane dubu daya da dari biyar sun kamu da cutar.

Wadansu kuwa, tuni sun sheka lahira, sa'o'i kadan bayan kamuwa da cutar.

Cutar ta yadu ne zuwa kauyukan dake arewacin birnin, lamarin da ya haifar da cunkoso a asibitocin yankin.

Asibitoci sun cika makil da mutanen wadanda ke fama da matsanancin zazzabi, da amai da gudawa.

Ba dai a tabbatar da haka ba, amma fargabar itace wannan mafari ne a annobar cholera a kasar.

Kungiyoyin lafiya na kasa da kasa na ta faman kokari wajen ganin sun shawo kan cutar domin kada ta sake bazuwa a sauran sassan birnin na Port au Prince inda dubban mutane suka yada zango a sansanoni a sanadiyar girgizar kasar da aka yi a watan Junairun da ya gabata.