Isra'ila tana kara gina gidaje a filayen Falasdinawa

gini a yankin Falasdinawa da aka mamaye
Image caption An linlinka yawan gine-gine a filayen Falasdinawa

Wata Kungiya a Israila ta ce, tun bayan dage dokar hana gine gine a yankunan da Yahudawa suka mamaye, sabbin gidajen da ake ginawa a yanzu sun lunka har sau hudu a kan yawan wadanda aka gina a can baya.

Wani mai magana da yawun kungiyar wadda ake kira Peace Now, ya ce a watan da ya wuce kadai, an fara gina sabbin gidajen Yahudawa 600 a yankunan Palasdinawan da aka mamaye.