Maleriya na kashe Indiyawa fiye da dubu 200

Daya daga cikin masu fama da maleriya a Indiya
Image caption Daya daga cikin masu fama da maleriya a Indiya

Wani sabon bincike ya nuna cewa yawan mutanen da zazzabin cizon sauro, wato maleriya, ke kashewa a Indiya ya haura yadda aka kiyasta a baya nesa ba kusa ba.

Sakamakon binciken, wanda mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ta wallafa, ya nuna cewa yawan mutanen da cutar ke kashewa ya nunka kiyasin Kungiyar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, wato WHO, har sau goma sha uku.

Ita dai WHO ta ce duk shekara mutane dubu goma sha biyar ne ke mutuwa a kasar ta Indiya sakamakon kamuwa da zazzabin na cizon sauro.

To amma wannan kididdiga ta baya-bayan nan ta nuna cewa yawan wadanda ke mutuwa ya haura dubu dari biyu.

Hakan kuma ya jefa shakku a kan alkaluman yawan wadanda ke mutuwa sanadiyyar zazzabin na cizon sauro a fadin duniya.

Yayin gudanar da wannan bincike dai kwararraun ma'aikatan lafiya sun yi hira da iyalai ne inda suka bukace su su siffanta yanayin rasuwar danginsu.

Da likitoci suka yi nazari a kan bayanan da aka tattara kuma sai suka tabbatar da cewa maleriya ce ta haddasa mutuwar.

Kungiyar ta WHO dai ta amsa cewa kididdigar ta na da tawaya, to amma ta ce wadannan alkaluman sun wuce kima.

A cewarta, wadansu cututtukan ma ka iya haddasa irin zazzafan zazzabin da maleriya ke haddasawa, wanda ke kaiwa ga mutuwar marasa lafiya.