Amos Adamu ya ce bashi da laifi

Amos Adamu
Bayanan hoto,

Amos Adamu

Daya daga cikin jami'an hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, da aka zarga da yunkurin cinhanci, Dr Amos Adamu wanda ya fito daga Najeriyar, ya shaidawa BBC cewa bai aikata wani laifi ba.

Wata jaridar Burtaniya ce dai ta zargi Amos Adamu, wanda dan kwamitin gudanarwa en na FIFA, da yunkurin sayar da kuri'arsa a kokawar da ake ta neman kasar da za ta dauki nauyin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 da 2022.

A ranar laraba ne dai hukumar ta FIFA ta dakatar da Mista Adamu na wucin gadi har sai an gama bincike.

A wata hira ta musamman da yayi da BBC, Dr Amos Adamu, wanda ke magana a karon farko tun bayan faruwar lamarin, ya ce yana maraba da binciken da kwamitin da'a na FIFA ke gudanarwa, wanda ya dakatar da shi daga shiga duk wasu al'amura na kwallon kafa har zuwa taron da kwamitin zai kara yi ranar 15 da 17 ga watan gobe.

Ya ce ;"ina murna da binciken, domin zai baiwa duniya damar sanin gaskiyar abin da ke faruwa.

"Ni a iya tunani na, ban aikata wani laifi ba kan abinda suke fada. Nasan kwamitin da'ar, kwamiti ne mai martaba, don haka ina fatan gaskiya za ta bayyana."

Mista Adamu ya kuma ce yana da tabbacin kwamitin zai wanke shi daga zargin da ake masa.

Ina da kwarin guiwa sosai, domin abin da aka bayyanawa duniya ba shi ne ainahin abinda ya faru tsakanina da 'yan jaridar ba.

Ba na so nace komai a game da kwamitin, domin suna bincike. Na amince da FIFA da kuma shugabanta, don haka wannan bincike zai warware zare da abawa. Ko da wakilin BBC ya tambayi Mista Adamu, cewa ko kwallon kafa harka ce ta marasa gaskiya?

Sai yaja dogon numfashi, sannan ya ce ba zance haka ba, wannan ba gaskiya bane.

Mr Adamu, wanda shi ne shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasashen yammacin Afrika, an ce ya gayawa 'yan jaridar da suka yi shigar burtu cewa, yana so a bashi dala dubu 800, domin gina wasu filayen wasa na zamani guda hudu ana Najeriya.

Wani kwamitin FIFA mai mutane 24, za su kada kuri'a a ranar 2 ga watan Disamba, domin zabar kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniyar a shekara ta 2018 da 2022, sai dai babu tabbas ko za a gudanar da zaben a ranar ko kuma a'a.