An kashe limamin unguwar Kandahar dake Bauchi

Bauchi
Image caption Najeriya

A Najeriya, rahotanni daga Jihar Bauchi na cewa a daren jiya wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun harbe wani mai unguwa har lahira.

Lamarin ya faru ne a Unguwar da ake kira Kandahar.

'Yan bindigar sun tarar da mai unguwar wato Malam Tukur na hira da wasu mutanen unguwa bayan an idar da sallar Isha, inda suka harbe shi har lahira.

Wasu wadanda abin ya faru a gabansu sun bayyana cewa mai unguwar ne ma ya jagoranci Sallar Isha'in da aka yi a daren jiya, kafin daga baya mutanen biyu da ke tafe a kafa su yi harbi sau uku.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa yanzu haka dai suna cikin yanayi na zaman dar dar, kuma tun daga wannan lokacin kowa ya shige gidansa ya rufe kofa.

Yanzu haka dai jami'an tsaro sun bazu a unguwar domin tabbatar da tsaro a unguwar.

Jihar bauchi dai ta sha fama da matsalar 'yan Boko haram ko da yake dai, kawo yanzu ba a san ko su wanene suka kai wannan hari ba.