Majalisar Dattawan Faransa ta yarda a kara shekarun ritaya

Nicolas Sarkozy, Shugaban Faransa
Image caption Nicolas Sarkozy, Shugaban Faransa

Majalisar dattawan Faransa ta amince da shirin gwamnati na kara shekarun ritaya daga 60 zuwa 62, shirin da ake ta takaddama akai.

Gwamnatin masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta takaita mahawarar, ta hanyar kada kuri'a daya tak kan gyare gyaran da 'yan adawa suka gabatar.

Wannan na nufin kenan a makon gobe, dukan bangarorin majalisar dokokin za su amince da kudirin dokar.

Sai dai kuma kungiyoyin kwadago sunce za su ci gaba da nuna adawarsu ga abin da suka kira: matakin da bai dace ba.

Shugaba Nicolas Sarkozy yace shirin na da muhimmancin gaske, wajen cike gibin kasafin kudin kasar.