Matasa a Nijeriya sun nemi Gwamnati ta tattauna da 'yan Boko Haram

Kungiyar matasan arewacin Nijeriya ta yi kira ga hukumomi kasar da su shiga sasantawa da kungiyar Boko Haram, kamar dai yadda suka yi da masu fafutukar Niger Delta, domin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake dangantawa da kungiyar a wasu jihohin arewacin kasarwar.

Matasan suka ce, ya kamata a magance yawan hasarar rayuka da tabarbarewar tsaro a Najeriyar, idan dai ana son kasar ta cigaba.