Wata kungiya a Najeriya ta ce Goodluck ya yi murabus

Henry
Image caption Henry Okah

A Najeriya wata kungiyar matasan kasar ta yi kira ga Speto Janar na 'yan sanda da ya gaggauta daukar mataki akan kungiyar MEND wadda ke fafutukar 'yanto yankin Niger Delta.

Wannan kira wanda suka yi a wata takarda da suka rubutawa Speto Janar din ta hannun kwamishinan 'yan sanda na Jihar Kano, ya biyo bayan tagwayen harin bama- bamai da aka kai Abuja a ranar da kasar ke bikin cika shekaru hamsin da samun yancin kai.

Kungiyar mai suna Arewa Citizen Action for Change ta kuma ce za ta dauki matakin shari'a domin ganin an tsige shugaban kasar Najeriya Dokta Goodluck Jonathan bisa abinda ta kira kokarin wanke kungiyar da ce itace ta dauki nauyin harin ranar daya ga watan Oktobar da muke ciki.

Sannan kuma ta kara da cewa idan har 'yan majalisar kasa ba su dauki matakin tsige shugaban kasa kan lamarin tsaro ba, to zasu kaddamar da wata zanga zangar sai baba ta gani ta mutane miliyan uku har sai shugaban ya sauka bisa radin kansa.

Kungiyar ACAC din dai ta ce ta dauki wannan matakin ne domin yiwa jami'an tsaro hannun ka mai sanda, ganin yanda ake tafiyar hawainiya wajen zakulo wadanda ke da hannu a harin.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai hukumar tsaro ta farin kaya wato SSS ta kasa ta gurfanar da wasu mutane bakwai a gaban kotu, ciki har da kanin Henry Okah wanda shi ma ya ke fuksantar tuhuma a kasar Afrika ta kudu, bisa zargin hannu a tagwayen hare haren da aka kai a Abuja.