Wani rahoto ya ce samun kasar Palasdinu zai yi wuya

Image caption Tattaunawar Gabas ta tsakiya

Wani rahoton hukumar kare hakkokin bil adama ta majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa cigaba da gina matsugunan yahudawa da Isra'ila ke yi a filayen Palasdinu abune da ba za'a iya mayar da hannun agogo baya ba.

Rahoton ya bayyana cewa gina matsugunan yahudawa da Isra'ilan ke yi a gabar tekun Jordan da kuma gabashin birnin kudus, ya yi matukar girmama a filayen Palasdinu.

Rahoton ya bayyana cewa da wuya kudurin kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya game da rage adadin gine gine a yankin Palasdinun da aka amince dashi a shekarar 1967, ya yiwu a halin da ake ciki a yanzu.

Wannan ce kuma madogarar da tattaunawar zaman lafiyar da ake yi a halin yanzu ta raja'a akai domin kafa kasar Palasdinawa mai cin gashin kanta.

To sai dai kamar yadda rahoton ke bayyanawa, wannan kamar mafarki ne, kuma da wuya a iya cewa yarjejeniyar zaman lafiyar da ake son cimmawa, na da wani tushe mai karfi.

Amma Isra'ila tuni ta mayar da martani inda ta ke cewa akwai son kai a cikin rahoton domin ba a ambaci su kuma irin harin ta'addancin da Palasdinawa ke aikatawa ba.