Kwalara ta kashe sama da mutum 200 a Haiti

Cutar amai da gudawa a kasar Haiti
Image caption Mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar amai da gudawa a kasar Haiti sun haura mutum dari biyu

Adadin mutanen da suka mutu a kasar Haiti sakamakon barkewar annobar cutar kwalara sun haura mutum dari biyu

Hakan na zuwa ne dai dai lokacin da hukumomin kasar ke kara kaimi wajen ganin sun hana yaduwar cutar zuwa Port-au-Prince, babban birnin kasar.

An samu rahotannin bullar cutar a wasu yankunan kasar baya ga yankin da cutar tayi kamari

Wata kakakin Majalisar Dinkin Duniya ta ce hana yaduwar cutar yanzu haka shine babban kalubalen da suke fuskanta.

Fiye da mutane miliyan daya ne da suka tsiri bayan mummunar girgizar kasar data abku a kasar a watan janairu ke zaune a wasu tantuna, yanayin da ake ganin yasa su saurin kamuwa da cututtuka dabam dabam.