'Yan bindiga sun hallaka matasa 13 a Mexico

Kashe Kashe a kasar Mexico
Image caption Rikici tsakanin kungiyoyin 'yan kwaya masu gaba da juna a kasar Mexico na sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kasar

Wasu 'yan bingida sun kashe akalla matasa goma sha uku a kasar Mexico a wani gida da suke bukin rawa a birnin Juarez.

Masu gabatar da kara sun ce 'yan bindigar sun isa gidan ne da daren jiya juma'a dauke da manyan bindigogi cikin wasu motoci uku inda suka bude wuta.

Akalla wasu mutane goma ne suka samu raunuka daban daban, inda jami'an 'yan sanda suka ce sun tsinci kwanson harsasai fiye da saba'in a wurin da al'amarin ya auku.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa BBC cewar daya isa wajen ya tarar 'yan bindigar sun dauki gawar wata mata cikin mota, yayin da wani matashi ke zaune a bayan motar.

Garin Juarez dai ya kasance wani fagen daga inda kungiyoyin 'yan kwaya masu gaba da juna ke rikici tsakaninsu a koda yaushe