Pentagon ta ce dama ta abinda ya faru a Iraqi

Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta bayyana cewa sam ba ta da wani shiri na sake bincikar cin zarafin da shafin yanar gizo na Wikileaks ya bayyana, cewa an yi a Iraqi.

Wani mai magana da yawon ma'aikatar ya shaidawa BBC cewa tuni sojin Amurka suka mikawa jami'an Iraqi rahotanni game da irin yanda sojoji da 'yan sandan Iraqin ke gallazawa fursunoni.

Ya kara da cewa bullar wadannan bayanan da ke kunshe da kimanin shafuka dubu dari hudu, ba zai sauya yanda Pentagon ta fahimci abubuwan da suke faruwa ba.

A wani rubutaccen jawabi da suka aikowa BBC, mai magana da yawon sojin Amurka Kanal Dave Lapan ya bayyana cewa tsarin Amurka game da yanda ake gallazawa da azabtarwa, irin tsari ne da ya dace da sharuddan majalisar dinkin duniya.

Ya jaddada cewa a lokacin da suka samu labarin cewa sojin Iraqi na azabtar da 'yan Iraqin, rawar da Amurka ta taka shine na sanya idanu da kuma mika batun zuwa gaba, wanda su kuma suka sanar da Jami'an Iraqin.

Kanal Lapan dai ya bayyana cewa wannan al'ada ce ta tsarin yarjejeniyar kasa da kasa.

Ya kara da cewa bayanan da shafin Wikileaks din ya bayyana, tuni manyan jami'an su sun samu damar gani tun ma kafin a kai ga haka, kuma suna daukar matakai akai.