Kotu ta nemi majalisa ta koma zama a Iraq

Kotun kolin Iraki ta umurci sabuwar majalisar dokokin kasar da ta koma zama, tana mai cewar, shawarar da majalisar ta yanke tun farko, ta dakatar da zaman nata har sai abinda hali yayi, ta sabawa tsarin mulkin kasar.

Tun babban zaben da aka gudanar a Irakin a watan Maris, sau daya kawai majalisar dokokin ta gana - watau lokacin da ta dakatar da yin duk wani zaman, har sai lokacin da 'yan siyasa suka amince da sabuwar gwamnatin da ake son kafawa.

A cewar wani wakilin BBC a birnin Bagadaza, ana sa ran hukuncin kotun kolin, zai tilastawa 'yan majalisar sake ganawa.

To sai dai ba yiwuwar zai kawo karshen kiki-kakan da ake fuskanta, game da batun rarraba manyan mukaman gwamnati