Najeriya ta ciri tuta wajen magance Polio

Polio
Image caption Rigakafin Polio

Gidauniyar Majalisar Dinkin Duniya da ke bayar da agaji ta fuskar yaki da cutukkan kananan yara a duniya, wato United Nations Foundation, ta yabawa Najeriya kan irin nasarar da ta samu wajen kawar da cutar Polio, wato shan inna a kasar.

Cutar Polio a baya, a kiyasi na gidauniyar UN Foundation, ta fi yin katutu a yankin Arewacin Najeriya, fiye da ko ina a duniya.

Shugaban Gidauniyar Sanata Timothy Rait a yayin wata ganawa da ya yi da Sarakuna a fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato, ya ce a cikin shekaru biyu a Najeriya, an samu raguwar adadin yaran da ke kamuwa da cutar Polio da kashi casa'in da takwas cikin dari.

Mr. Rait dai ya bayyana cewa a shekaru biyun da suka gabata, kimanin yara dari takwas ne suka kamu da cutar Polio a Najeriya, amma a bana bai fi yara takwas ne kadai suka kamu da cutar ba.

A yanzu haka dai Gidauniyar Majalisar Dinkin Duniyar na duba yiwuwar yakar cutar gaida a Najeriya, wadda ita ma ta ke salwantar da rayuwar yara ko nakasa su.