Kasuwar jarin Singapore za ta hade da ta Australia

stock market
Image caption Hada hadar hannayen jari

Kasuwar hada-hadar hannun jari ta Kasar Singapore ta yi tayin sayen takwararta ta Kasar Australia akan dala biliyan takwas da miliyan dari biyu.

Idan har aka amince da wannan yarjejeniyar, to wannan zai kasance hadin gwuiwar kasuwar hanayen jari na farko a nahiyar Asiya.

Kasuwar hada hadar Singapore din dai na so ne ta sake fadada cigaban da ta ke samu, wanda wannan na da nasaba da karuwar tattalin arzikin kasar Sin.

Kasuwar ta bayyana cewa za ta rage kashe kudade domin janyo hankalin masu zuba jari, da kuma kamfanonin da ke sha'awar bunkasa na su hannayen jarin.

Wannan mataki kuma zai taka wata mahimmiyar rawa wajen tabbatar da matsayar tattalin arzikin da kasuwar ta Singapore ke da shi a nahiyar Asiya.

Wani karin abu da zai ja hankalin masu zuba jari a kasuwar shine cewa, tsarin yanda ake tafi da kasuwar a bayyane ya ke dalla- dalla.

Kuma lallai ne cewa akwai yiwuwar masu jari da ga Australian su amfana ta hanyar samun damar kutsawa cikin kasuwannin nahiyar.