Wasu mahara sun kai hari ofishin 'yan sandan Yobe

Boko Haram
Image caption Rikicin Boko Haram

A Najeriya wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari wani ofishin 'yan sanda a Jihar Yobe dake Arewacin kasar.

Maharan akan babura guda bakwai, suna tafe suna kirarin Allahu Akbar, sun kai harin ne a ofishin 'yan sanda dake garin Bara Division.

Harin ya afku ne da misalin karfe biyu na daren jiya, inda aka kwashe kimanin sa'a guda su na fafatawa da 'yan sandan.

Daga baya ne kuma maharan su ka tsere bayan gari.

Hukumar 'yan sandan Jihar Yoben ta ce babu wanda ya rasu.

A kwanakin nan dai ana ci gaba da samun hare-haren da ake dangantawa da Boko Haram din a jihohin Bauchi da Borno da ke Najeriyar.