Karzai ya tabbatar da karbar kudi daga Iran

Hamid karzai
Image caption An dade ana zargin gwamnatin Afghanistan da cinhanci da rashawa

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai, ya tabbatar da rahotannin da ke cewa ofishinsa ya karbi kudi daga Iran, sai dai ya ce kudin na halal ne.

Mista Karzai na mayar da martani ne ga wani rahoto da jaridar New York Times ta wallafa, wanda ya ce Iran tana baiwa na hannun damar shugaban kudade.

Rahoton ya ce ana bada kudin ne domin karfafa ikon fada ajin da Iran ke da shi a kasar.

Da yake magana a wajen taron manema labarai, shugaban ya ce kasashe da dama suna baiwa Afghanistan kudi ta wannan hanya ciki harda Amurka.

"Gwamnatin Iran tana tallafa mana da Yuro dubu dari shida ko bakwai sau daya ko biyu a duk shekara, wannan taimako ne na kasa da kasa," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya ce jagoran ma'aikatansa, Umar Daudzai, "shi ya ke karbar kudin a madadina."

Mista Karzai ya ce kasashe da dama na baiwa kasar kudi domin tallafawa ofishin shugaban kasa tafiyar da ayyukansa.