EFCC ta yi gargadin hana tsayarda wasu 'yan takara

Image caption Shugabar Hukumar EFCC, Mrs Farida Waziri

A Najeriya, hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta aikewa jam'iyyun siyasar kasar jerin sunayen wadansu mutane, ciki har da wasu fitatun 'yan siyasa tana bukatar jam'iyyun su hana su tsayawa takara a zabukan 2011.

Ko da yake hukumar ta EFCC ta ce ba ta da hurumin haramtawa wata jam'iyya tsayar da wani mutum takara, a cewarta ya rage ga jam'iyyun su yankewa kansu shawara ko ya dace su tsayar da wani wanda ke cikin jerin sunayen.

Sai dai wasu 'yan siyasar da abin ya shafa sun yi watsi da wannan bukata ta hukumar EFCC suna masu cewa tastuniya ce kawai.

Hukumar ta EFCC dai ta taba fitar da jerin sunayen mutanen da ta ce ta haramtawa yin takara ana gab da zabukan 2007, al'amarin da ya jawo cecekuce a kasar.

Hukumar ta EFCC dai ta wallafa sunayen mutanen fiye da dari ne a shafinta na intanet, cikinsu kuma har da wasu fitattun 'yan siyasar kasar, ta kuma nemi jam'iyyun siyasa kada su tsayar da su takara.

Image caption Taswirar Najeriya

Daga cikin 'yan siyasar da EFCC ta wallafa har da tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar DPP a zabukan 2007, Alhaji Attahiru Bafarawa.

Da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Saminu Turaki, da tsohon gwamnan jihar Filato, Cif Joshua Dariye, da kuma tsohon Ministan Babban birnin tarayya, Malam Nasir El Rufai.

Sauran wadanda ke cikin jerin sunayen sun hada da tsohon gwaman Jihar Adamawa, Mista Boni Haruna, da takwaransa na jihar Taraba, Reverend Jolly Nyame.

Har ila yau akwai tsohon gwaman jihar Abia kuma dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PPA a shekarar 2007, Cif Orji Uzor Kalu, da kuma tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP a yankin kudu maso yamma, Cif Bode George.

Sai dai hukumar ta EFCC ta ce ba ta da hurumin da za ta haramtawa wani mutum tsayawa takara a zabukan na 2011.

Bamu da yancin hana tsayawa takara

Femi Babafemi kakakin hukumar ya ce; "Don debe duk wani shakku barin fara da cewa hukumar EFCC ba ta da hurumin haramtawa duk wani dan takara tsayawa zabe.Abu na biyu kuma shi ne wani jerin sunayen na mutanen da hukumar ta kai gaban kotu a bisa tuhumar cin hanci da rashawa kuma ya kasance a shafin hukumar na intanet tun shekarar 2008.Sai dai kawai a kan sabunta shi daga lokaci zuwa lokaci; ya rage ga duk wani mai bukata ya yi amfani da bayanan da ke ciki."

A shekarar 2007 ma dai Hukumar ta EFCC ta fitar da sunayen wasu mutane da ta ce an haramta musu tsayawa takara saboda tuhumarsu da ta keyi da cin hanci da rashawa, al'amarin da ya jawo cecekuce da kuma zarge-zargen cewa gwamnatin da ke mulki a wancan lokacin na amfani da hukumar don kawar da wadanda ke adawa da ita.

To amma Mista Babfemi ya ce wannan karon ba haka al'amarin ya ke ba.

"Kwata-kwata jerin sunayen na yanzu bai yi kama da na wancan lokacin ba. A wancan lokacin sunayen na mutanen da aka haratawa tsayawa takara ne wadanda wasunsu ma ba a tuhume su da wani laifi ba".

Amma jerin sunayen na yanzu na mutanen da ke fuskantar tuhuma ne a kotu kuma babu inda aka ce an haramta musu tsayawa takara.

Saboda haka idan jam'iyyun suna ganin bai dace su tsayar da wanda bai wanke kansa daga tuhuma ba, to ya rage nasu."

Tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Adamu, na cikin wadanda hukumar ta EFCC ta ambaci sunyensu, ya kuma shaida wa BBC ta waya cewa:

"Babu inda aka nuna a dokar kasar nan cewa idan an kai mutum kotu, ba zai iya tsaya takara ba. Sai kotu ta same ka da laifi ne za'a iya hana mutum tsayawa takara."

"Ni dan takara ne kuma da ikon Allah zan tsaya takara." A baya dai hukumar ta EFCC ta sha alwashin tabbatar da cewa mutanen da aka samu da laifin cin hanci da rashawa ba su sake hayewa kujerun mulki a Najeriya ba.

To amma abin da 'yan Najeriya za su jira su gani shi ne ko jam'iyyun siyasar kasar za su yi amfani da wannan shawara ta EFCC ko a'a.