Mutane 6 sun mutu a rikici da ya barke a wani kauyen dake jihar Filato

Rikici a jahar Filaton Najeriya
Image caption Wani sabon rikici ya barke a kauyen Ruwanko dake karamar hukumar Bassa a jahar Filato dake arewacin Najeriya

Hukumomin tsaro a jihar Filato sun tabbatar da mutuwar mutane shidda tare da jikkata wasu a wani hari da aka kai a kauyen Reweienkwu dake karamar hukumar Bassa.

Maharan dai sun yi kawanya ne kawanya jiya da dare, kuma harin ya biyo bayan wani lamari da ya auku ne a kauyen Gero daka karamar hukumar Jos ta Kudu inda mutum guda ya rasa ransa kana aka kashe shanu da dama.

Jihar Filato dai ta sha fama da tashe-tahen hankula a yan shekarun nan kuma kawo yanzu babu mutum guda da aka hukunta sabo da hannu a tashe-tashen hankulan.

Kakakin rundunar hadin gwiwa na wanzar da zaman lafiya a jahar Filaton Lt Col. Kingsley Umoh ya shaidawa BBC cewar suna kan binciken musabbabin rikicin yanzu haka, da kuma gano yawan mutanen da suka rasa rayukansu.

Ba'a dai taba samun barkewar tashin hankali a wannan yanki ba sai yanzu.

Jahar Filato dai tayi fama da rikice rikice a baya, abinda yayi sanadiyyar asarar rayuka da dama da kuma dukiya bila adadin