'Yan bindiga sun harbe masu shan kwaya a Mexico

Wasu 'yan bindiga a Mexico sun harbe wasu masu shan miyagun kwayoyi har lahira, su goma sha uku, a wani wurin da ake yi masu maganin daina shan kwayar, a kusa da Tijuana, kusa da kan kiya da Amurka.

Babu dai cikakkar masaniya a kan dalilin harbin, amma ana ganin yana da alaka da rin zubar da jinin da ake samu tsakanin kungiyoyin sayar da miyagun kwayoyi, wanda a halin yanzu ya yi kamari a kasar ta Mexico.