Kungiyar kare hakkin dan adam ta soki kasar Morocco

Kungiyar Human Rights Watch
Image caption Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch na zargin gwamnatin kasar Morocco da muzgunawa masu tada kayar baya a kasar

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta soki kasar Morocco da ci gaba da kamewa tare da tsare masu tada kayar baya a wasu haramtattun wuraren da ake tsare mutune.

A wani sabon rahoto data fitar, kungiyar ta ce hakan ya sabawa dokokin kasar da aka shimfida da nufin kare mutane tare da hana muzguna masu ba tare da bin ka'idoji ba.

Sai dai a nata bangaren gwamnatin kasar Moroccon tayi watsi da rahoton, tana mai cewa tsarin shari'ar kasar yana mutunta hakkin dan adam.