FIFA ta ware mutane 23 don zaben zakaran kwallon duniya

Tawagar Spain
Image caption Yan wasan Spain na daga cikin wadanda suka mamaye sunayen

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar da jerin sunayen 'yan kwallo 23 da za a zabi zakaran dan kwallon duniya na bana a cikinsu.

Sunayen wadanda aka dade ana jira, sun kunshi 'yan wasan da suka fi taka rawar gani a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a Afrika ta Kudu.

Yayinda 'yan wasan Spaniya da suka lashe gasar da kuma na Jamus da suka zo na uku suka mamaye jerin sunayen 23.

Shahararru daga cikin 'yan wasan sun hada da mai rike da kanbun Lionel Messi na Argentina, da Cristiano Ronaldo da Portugal da Wesley Sneijder na Holland da Andres Iniesta na Spain da Thomas Mueller na Jamus da Diego Forlan na Uruguay da kuma Asamoah Gyan na Ghana.

'Babu dan Ingila ko daya'

A karo na biyu a tarihi, bikin zai kunshi kyautar kwallon da ta fi kowacce kyau tare da sauran kyaututtuka daban daban da aka saba bayarwa.

Babu dai dan wasan Ingila ko kwaya daya da ya fito a jerin 'yan wasan da FIFA ta fitar.

Abinda yasa masu sharhi kan al'amuran wasanni ke ganin wata alamace da ke nuna irin koma bayan da kungiyar kwallon kasar ta (Three Lions) ke ci gaba da fuskanta.

Image caption Diego Forlan ne ya zamo dan wasan da yi fi kowanne a gasar cin kofin duniya

Yan wasa uku ne dai suka samu shiga daga gasar Premier ta Ingila, wadanda suka hada da Didier Drogba na Chelsea da Cesc Fabregas na Arsenal da Asamoah Gyan na Sunderland.

Za a sanar da zakaran dan kwallon na duniya a ranar 10 ga watan Janairu na shekara ta 2011, a wani biki da za a gudanar a hedkwatar hukumar FIFA da ke birnin Zurich na kasar Switzerland.

Jerin sunayen 23

Xabi Alonso (Spain) Dani Alves (Brazil) Iker Casillas (Spain) Cristiano Ronaldo (Portugal) Didier Drogba (Ivory Coast) Samuel Eto'o (Cameroon) Cesc Fabregas (Spain) Asamoah Gyan (Ghana) Julio Cesar (Brazil) Miroslav Klose (Germany) Philipp Lahm (Germany) Maicon (Brazil) Thomas Mueller (Germany) Arjen Robben(Netherlands) Bastian Schweinsteiger (Germany) David Villa (Spain) Xavi (Spain) Carles Puyol (Spain) Andres Iniesta (Spain) Diego Forlan (Uruguay) Lionel Messi (Argentina) Mesut Oezil (Germany) Wesley Sneijder (netherlands).