Hukumar SSS ta kama makamai a Lagos

A Najeriya Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta ce ta cafke kwantena goma sha uku a jihar Lagos, wadanda kuma bayan ta bude guda daga ciki ta samu Makamai da suka hada da roka da gurneti da kuma alburusai.

Mataimakiyar daraktan hulda da jama'a ta Hukumar Mrs Merilyn Ogar ta shaidawa BBC cewar an shigar da makaman cikin kasar bayan an boye su cikin kwantenar a matsayin kayan gini.

Mataimakiyar Daraktan Hukumar tsaro ta farin kaya Mrs. Marilyn Oga ta shaidawa BBC cewar Hukumar ta samu bayanan shigo da makaman ne, abin da kuma ya sa ta cafke kwantena goma sha ukun da aka shiga da su ta tashar jirgin ruwa dake Apapa a lagos.

Mrs Ogar ta ce an boye makaman ne da nufin cewar kayan gini ne, amma bayan jami'an hukumar sun bude daya daga cikin kwantenan mai dauke da akwatuna ashirin da hudu an gano makamai a cikin wasu daga cikin akwatunan.

Ta ce bayan an bude akwatuna goma sha biyu, an samu gurneti da makamin harba roka da kuma alburusai a akwatuna takwas, a yayinda aka ga tiles din da ake sanyawa a daki a akwatuna hudu.

A dai dai lokacin da nake hada wannan rahoton hukumar ta ce tana ci gaba da bude sauran kwantenan ne domin ganin abubuwan dake ciki.

Mrs Marilyn Ogar dai harwayau taki ta bayyana kasar ta kwantenar ta fito ko kuma inda za'a kai makaman a cikin Najeriya, saboda ta ce hukumar na ci gaba da bincike ne.

Jami'ar ta ce Hukumar ta cafke wasu mutane game da al'amarin kuma tana ci gaba da tsananta bincike tare da hadin gwiwar 'yansandan kasar da kuma jami'an tsaro.

Mrs Marilyn Oga dai ta ce hukumar za ta gana da manema labarai idan ta kammala binciken ta.

Wannan lamari dai ya zo ne adaidai lokacin da ake ci gaba da nuna shakku kan yanayin tsaro a kasar, ganin harin bom din da aka a ranar da kasar ke bikin cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai, da kuma hare haren sari ka noke da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kaiwa a wasu jihohin arewacin kasar.