tsohon shugaban Argentina, Kirchner ya rasu

Nestor Kirchner
Image caption Mr Kirchner ya yi fama ne da bugon zuciya

Allah ya yi wa tsohon shugaban kasar Argentina, Nestor Kirchner rasuwa ta sanadiyyar bugun zuciya.

Mr Kirchner mai shekaru sittin da haihuwa kuma mai gidan shugabar kasar ta yanzu Cristina Fernandez Kirchner ya rasu ne a asibiti ba zato ba tsammani.

A shekara ta 2007 ne Cristina Fernandez Kirchner ta karbi ragamar mulkin kasar daga hannun mai gidanta, bayan kasar ta farfado daga koma bayan tattalin arzuki.

An dai yi ta sa ran zai sake tsayawa takarar shugaban kasa, duk da kayen da jam'iyyarsa ta sha a zaben majalisar dokokin kasar.