'Yan majalisar Faransa sun amince da sabon tsarin pensho na kasar

Zauren majalisar dokokin Faransa
Image caption Zauren majalisar dokokin Faransa

Majalisar wakilai ta kasar Faransa ta kada kuri'ar amincewa da shirin dokar nan da ya haifar da kace-nace, wanda a karkashinsa zaa kara shekarun yin ritaya daga 60 zuwa 62.

Yan Majalisar 335 ne suka kada kuru'ar amincewa yayin da yan Majalisa 233 suka kada kuru'ar kin amincewa da dokar.

Kasar ta Faransa dai ta fuskanci zanga- zanga da dama daga kungiyoyin kwadago wadanda ke adawa da gyaran.

A yanzu zaa tura wannan doka ga Shugaban Kasa wanda ake sa ran zai sa ma ta hannu domin ta fara aiki daga watan Nuwamba mai zuwa.