Mutane 272 ne suka hallaka a Indonesia

Wasu jerin bala'oi sun afkawa kasar Indonesia
Image caption Ana ci gaba da aikin ceto mutanen dake da sauran numfashi a kasar Indonesia

Mahukunta a Indonesia sun ce adadin mutanen da suka hallaka a bala'o'in da suka afkawa kasar ya kai 272. Masu aikin agaji a tsibirin Mentawai sun ce har yanzu ba a ji duriyar mutane 412 ne, kwanaki biyu bayan afkuwar girgizar kasa mai dauke da igiyar ruwa ta tsunami a yammacin Sumatra.

Mahukunta suka ce an samu matsala wajen gargadin da aka yi wa jama'a na su kauracewa gidajensu.

Jami'an hukumar gudanarwar Yammacin Sumatra sun ce jirage masu saukar ungulu sun samu kaiwa ga wasu daga cikin kauyukan da ke tsibiran Mentawai.

Sai dai har yanzu babu tabbas a kan irin barnar da ta auku saboda har yanzu kungiyoyin agaji na ta fafutukar kaiwa ga wuraren da barnar ta fi tsanani kuma har yanzun ba su samu damar tuntubar mutanen akalla kauyuka 13 da ke bakin gaba.

'Zan koma gida'

Shugaban kasar ta Indonesia wanda ke halartar wani taron koli na kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya a Vietnam, ya janye daga taron don kai ziyara a tsibiran na Mentawai.

Ya shaida wa mahalatta taron cewa: "Zan je gida don tabbatar da cewa ayyukan agaji na gaggawa suna tafiya yadda ya kamata kuma in Allah Ya yarda zan dawo wajen taron don karbar shugabancin kungiyar a madadin Indonesia daga Vietnam".

Jami'ai sun ce abin da suka sa a gaba yanzu shi ne kokarin gano wadanda suka tsira da rayukansu da kuma gina matsugunai na jeka-na-yi-ka nesa da gaba ko da za a sake samun girgizar kasar.

A halin da ake ciki kuma, a yankin Java, jami'ai na na ta kokarin kwashe mutane daga kewayen tsaunin Merapi.

Masana dai sun yi kashedin cewa ko da yake tsaunin ya daina yunkuri, akwai yiwuwar zai sake yin amai.