Majalisar dokokin Najeriya zata kada kuri'a akan gyaran kundin mulki

Shugaban Hukumar zaben Najeriya farfesa Attahiru Jega
Image caption 'Yan Majalisar dokokin najeriya zasu kada kuri'arsu akan gyare gyaren da akai wa kundin tsarin mulkin kasar da zai bada damar dage lokacin zabe

Majalisar dokokin Najeriya zata kada kuri'a akan gyare-gyaren da aka yiwa kundin tsarin mulkin kasar dangane da bukatar hukumar zabe na samun karin lokacin shirya zabe mai inganci a badi.

Wannan dai shine matakin kusa da na karshe a kokarin baiwa hukumar zaben kasar karin lokacin da take bukata don kintsawa zaben na shekarar 2011.

'Yan majalisar dokokin dai zasu kada kuri'arsu ne akan wasu gyare gyare da suka haka da gudanar da zaben tsakanin kwanaki dari da hamsin zuwa talatin kafin wa'adin wadanda aka zaba ya cika.

Haka kuma 'yan majalisar zasu kada kuri'a akan batutuwan da suka shafi kararrakin zabe

Nan da makon farko na watan gobe ne dai ake saran mikawa majalisun dokokin jahohi 36 na najeriya wadannan gyare gyare domin su ma su amince