Shekaru 11 da kaddamar da shari'a a jahar Zamfara

Ahmed Sani
Image caption Ahmed Sani Yarima ne ya fara kaddamar da tsarin shari'ar

A ranar laraba ne ake cika shakaru goma sha daya da kaddamar da aiki da tsarin shari'ar musulunci a jahar Zamfara dake arewacin Najeriyar inda daga bisani wasu jahohi a kasar suka bi sahu.

Akasarin jihohin da suka kaddamar da tsarin shari'ar musuluncin dai sunce sun fito da shi ne da nufin kyautata halayya da yanayin rayuwar al'umominsu.

A ranar 27 ga watan Oktoban 1999 ne, gwamnan jihar Zamfara na wancan lokacin Alhaji Ahmed Sani Yariman Bakura, ya kaddamar da shari'ar a jihar ta Zamfara.

Kaddamar da shari'ar dai ya jawo kace-nace tsakanin masu goyon baya da kuma adawa, abinda ya haifar da rikici a wasu sassan Najeriya.

Sai dai hakan bai sanya gwamnatin jihar ta wancan lokaci sauya tunani ba, saboda a cewarta ta yi hakanne domin kyautata rayuwar jama'a.

Nasara ko rashinta

Kuma daga bisani wasu jihohin kasar 11 sun bi sahunta, sakamakon bukatar hakan da jama'ar jihohin suka nuna.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Wakilin BBC a jihar Zamfara Haruna Shehu Tangaza, ya ce ra'ayoyi sun banbanta kan yadda tsarin shari'ar ya gudana a cikin shekarun 11, musamman a zamfara wacce akewa kallon abin koyi ta wannan fuska.

Malam Sanusi Muhammad Kwatarkwashi, shugaban gammayyar kungiyoyin musulmi a jihar ta Zamfara, ya ce an samu nasarori da dama.

"Irin fasadin da ya kasance yana gudana ada yanzu ya kau, koda mutum zai yi sai dai a boye, kusan duk yaran da ya tashi shekaru goma da suka wuce bai san wani abu mai suna gidan karuwai ba."

'A kotuna kawai akeyin shari'ar'

Ya kara da cewa: "Mun sha samun matan aure da suke zuwa suna godiya kan cewa tsarin shari'a yasa mazajensu sun sauya halinsu, suna kwana a gida, suna kumakyautata musu."

Image caption Wasu jahohi da dama a Najeriya sun bi sahun Zamfara wajen kaddamar da tsarin shari'a

Sai dai wasu na ganin tsarin shari'ar a tsawon wannan lokacin ya kare ne a kan talaka, kamar yadda wannan malamin da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa BBC:

"Sanda aka fara kaddamar da shari'a mutane sun zaci batun cinhanci ya kau, amma daga baya sai ya zamo a kotuna kawai akeyin shari'ar, banda ofisoshin gwamnati da kuma na 'yan siyasa."

A yanzu da ra'ayoyi suka banbanta kan yadda tsarin ke tafiya, kalubalen da ke gaban mahukunta shi ne na tabbatar da cewa kwalliya ta biyan kudin sabulu ganin irin makudan kudaden da ake warewa wannan fanni da kuma fatan da jama'a ke da shi a kan lamarin.