Amnesty ta soki shirin Gwamnatin jahar Rivers

Kungiyar Amnesty International
Image caption Dubban mutane ne zasu rasa matsuguni matukar gwamnatin jahar Rivers ta aiwatar da shirinta na rusa gidajen da suke bakin ruwa a birnin Fatakwal

Kungiyar kare hakkin Bil'adama ta Kasa da Kasa, Amnesty International ta yi gargadin cewa dubban mutane ne ka iya rasa matsuguni sakamakon gine gine da ake shirin yi a birnin Fatakwal, a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur a Najeriya.

Hukumomi dai sun ce suna shirin rusa gidajen dake kusa da bakin ruwa ne don samun filin da zasu gina otel otel da shaguna da kuma gidajen cinema.

Sai dai Kungiyar ta Amnesty ta ce yin hakan ka iya jefa dubban jama'a cikin wani mawuyacin hali domin akasarin mutanen ba su da inda zasu je matukar aka rusa gidajen su.

Kungiyar ta Amnesty tayi gargadin cewa kimanin mutane dubu dari biyu ne zasu iya rasa matsugunai matukar ba'a tanadar musu da gidajen da zasu zauna ba.