Shugabannin Turai na taro a Brussels

Shugabannin Turai na taro a Brussels
Image caption Ana saran yin zazzafar muhawara a wajen taron

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai na taro a Brussels, domin duba yiwuwar daukar tsauraran matakai kan kasashen da suka sake fadawa cikin matsalar gibi da kuma dimbin bashi.

Duk da cewa kasafin kudin tarayyar na badi ba ya cikin agendar taron, Burtaniya na neman sauran kasashe da su yi watsi da karin kashi 5 da digo 9 cikin dari da 'yan majalisar tarayyar suka amince da shi.

A wannan lokacin da ake matse bakin aljihu, akwai yiwuwar a amince da karin da ya zai kai na kashi 2 da digo 9 cikin dari.

Sai dai ana saran samun rudani kan kudurin da ake son gabatarwa na janye damar kada kuri'ar da kasashen da suka fada cikin matsala irin su Girka ke da ita.

Kudurin wanda Faransa da Jamus suka gabatar, na nufin sai an sake rubuta kundin yarjejeniyar Lisbon, wacce da kyar aka amince da ita.

Kudurin wanda aka yiwa lakabi da Deauville Deal ( bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Faransa da Jamus), su kadai suka amince da shi ba tare da sauran shugabannin kungiyar ba.

Su dai shugabannin na shirin tafka muhawara ne kan rahoton da wani kwamitin cika aikin tarayyar ya gabatar, na yadda za a karfafa hanyoyin kula da tattalin arzikin tarayyar.