Jirage zasu fuskanci cikas wajen sauka a Paris

Zanga zangar kungiyoyin ma'aikata a kasar Faransa
Image caption Jiragen da zasu sauka a filin tashi da saukar jirage na Paris zasu gamu da cikas sakamakon shigar ma'aikatan filin jirgin cikin wani jerin gwano a karo na bakwai a yau

Kungiyoyi ma'aikata a Faransa sun sake yin kiran da a gudanar da zanga zanga kan sauye sauyen da gwamnatin kasar ke shirin yi akan batun pansho, duk kuwa da amincewa da kudirin dokar da majalisun dokokin kasar suka amince akai.

Kungiyoyin sun ce zasu ci gaba da gudanar da zanga zanga da jerin gwano a fiye da garuruwa dari a cikin kasar, wanda kuma ake saran zai kaiwo cikas ga zirga zirgar ababen hawa.

Ana saran jiragen da zasu sauka a filin tashi da saukar jirage na birnin Paris zasu gamu da cikas sanadiyyar shigar ma'aikatan filin tashi da saukar jiragen cikin wani jerin gwanon

Wani batu da yake dagawa gwamnatin kasar hankali a yanzu haka dai shine matatun man kasar dake cigaba da kasancewa a rufe