Ana kara kamuwa da cutar gubar dalma a Zamfara

Wuraren hakar dalma
Image caption Gubar dalma ta kashe yara da dama a jihar ta Zamfara

Jami'an kiwon lafiya na kasa da kasa dake jahar Zamfara a Najeriya, sun ce har yanzu ana samun yaran da ke kamuwa da cututtuka sakamakon shaker gubar dalma a wasu kauyukan jahar.

Hakama an kara gano wadansu kauyukan da suka gurbata da gubar bayan guda bakwai din da aka sani tun daga farko.

Sai dai hukumomin lafiya na kasa da kasa sun shaidawa BBC cewa kawo yanzu babu wanda ya rasu a cikin wadanda suka kamu da cutar a baya-bayan nan.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin jahar suka ci gaba da aikin share kauyukan da suka gurbata da gubar bayan dakatarwa ta kimanin watanni uku.

Wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza da ya ziyarci yankin Anka daya daga cikin yakunan da matsalar ta shafa, ya ce hukumomin kasa da kasa na ci gaba da tallafawa wadanda abin ya shafa.

Jami'ar hukumar a yankin ta shaida wa BBC cewa a watan Oktoban nan da ake ciki, babu wani yaro da cutar ta kashe, sai dai ta ce akwai yara kusan 500 da suke karkashin kulawar su.

A nata bangaren, gwamnatin jihar ta nemi gwamnatin tarayya da ta kawo mata dauki kamar yadda ta nema, idan har anaso a kawar da matsalar baki daya.