An danganta balain malalewar man amurka da rashin kyawun siminti

Malalewar mai
Image caption Wata hukumar bincike ta danganta bala'in malalewar man da aka samu a Amurka da rashin kyawun simintin da akai amfani da shi

Wata hukuma da shugaban Amurka Barrack Obama ya kafa don binciken matsalar malalan man data abku a tekun Mexico, ta ce mai yiwuwa amfani da aka yi da siminti wajen like rijiyar man tun da farko ya taimaka wajen abkuwar bala'in.

Hukumar ta ce kamfanin BP da ya mallaki rijiyar man da kuma kamfanin da yayi kwangilan yin simintin Halliburton, sun san cewa akwai matsala wajen kwaba simitin makwanni kafin rijiyar ta fashe

Rahoton hukumar ya bayyana cewa yayin da kamfanin Haliburton ya mika sakamakon wani gwaji da yayi ga kamfanin na BP akan simintin, mai yiwuwa ya aje wasu sakamakon bai mikawa kamfanin ba.

Kamfanin Halliburton dai ya musanta zargin da ake masa

Wannan al'amari dai shine yayi sanadiyar mutuwar ma'aikata 11 tare da haddasa bala'i ta fuskar muhalli da Amurka bata taba ganin irinsa ba.