EU ta amince da kafa wani asusu na dindindin

Shugabannnin kasashen EU
Image caption Shugabannnin kasashen EU sun amince da tsaurara ka'idojin nahiyar da kuma samar da wani asusu na din din din

Shugabannin kasashen Turai sun amince akan wata yarjejeniya da zata karfafa ka'idojin nahiyar turan da kuma samar da wani asusu na din-din-din da za'a yi amfani dashi na tunkarar duk wani rikici a nahiyar.

Sai dai yarjejeniyar zata hada da canje canje ga yarjejeniyar Lisbon.

Za kuma a kafa wani asusu na din-din-din don taimakawa kudin Euro a lokutan abkuwar duk wata matsalar tattalin arziki.

Sai dai idan har za'a samar da wannan asusun, kasar Jamus ta hakikance cewar sai fa idan har za'a aiwatar da wasu gyare gyare ga yarjejeniyar nan ta Lisbon.