Indonesia ta yi karin haske kan aukuwar bala'in tsunami

Wasu da bala'in na Tsunami ya ritsa da su.
Image caption Wasu da bala'in na Tsunami ya ritsa da su.

Wata jami'ar gwamnatin Indonesia ta ce cibiyar girgizar kasar da ta haddasa mummunar igiyar ruwan nan ta Tsunami a gabar ruwan Sumatra, tana kusa da doron kasa ne sosai saboda haka shirin nan na gargadin jamaa kafin aukuwar bala'in bai yi wani amfani ba.

Kusuma Habir, wadda jami'a ce a ma'iakatar harkokin wajen kasar, ta ce cibiyar girgizar kasar tana da nisan kilomita 80 ne daga tsibiran Mentawai.

Ta ce saboda haka ne igiyar ruwan ta cimma gabar teku cikin sauri ta yadda na'urar gargadi da shirin ke amfani da ita ba ta iya tura rahoto ba.

Mutane fiye da dari 4 ne dai aka tabbatar sun rasa rayikansu, wasu karin da dama kuma suka bace a sakamakon bala'in.

A halin da ake ciki kuma, mummunan yanayi na kawo cikas wajen aikin ceto da na kai agaji zuwa yankunan da abun ya shafa.