Kimanin mutane ashirin da biyar sun rasu a Iraqi

'Yan sanda a Iraqi sun bayyana cewa akalla mutane ashirin da biyar ne suka rasu, yayinda wasu kimanin saba'in suka ji raunuka bayan da wani dan kunar bakin wake ya tada bam a wani dakin shan shayi.

Bam din ya tashi ne a garin Balad Ruz, inda mafi yawan mabiyan akidar Shi'a ke zaune, a yankin arewa maso gabashin birnin Bagadaza.

'Yan sanda sun bayyana cewa dan kunar bakin waken sanye da rigar bama bamai, ya shiga dakin shan shayin ne da misalin karfe tara na daren jiya, inda ya tada bam din.

Dakin shan shayin kan kasance a cike makil da jama'a, suna hutawa, bayan dawowa daga kwadagon ranar.

Yankin Balad Ruz dai, wato in da bam din ya tashi, wuri ne da yawanci mabiya akidar shi'a ke zaune.

Ana alakanta wannan harin da wadanda suka faru a baya, makamantan wannan da cewa aikin mabiyar akidar sunni ne, domin takalar fada.

Sai dai kuma hare hare irin wannan sun ragu a Iraqi.

Na baya- baya da aka kai a birnin Bagadaza shine kimanin wata guda da ya gabata.