Kokarin ceto Tabkin Chadi daga kafewa

Yaran Chadi
Image caption Yaran Chadi

Manyan jami'ai na kasashen yankin Tabkin Chadi na duba hanyoyin da ya kamata a bi, domin ceto tabkin daga kafewa.

Kwararru daga kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru, Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da kuma Chadin, suna yin taro a birnin N'Djamena, domin yin nazari akan hanyoyin neman samar da ci gaba mai dorewa ga tafkin Chadin, wanda yake fuskantar matsalar kafewa a yanzu haka.

Fiye da mutane miliyan 30 da suke rayuwa da ruwan tafkin sun shiga cikin wani mawuyacin hali.

Bincike ya nuna cewa, har idan ba a samu shawo kan wannan matsala ba, nan da wasu shekaru masu zuwa ruwan tafkin zai kafe baki daya.

A cikin shekaru 50 da suka gabata fadin tafkin Chadin ya ragu daga kilomita dubu 25 murabba'i, zuwa dubu 2500.