Hukumomin Najeriya na son rage yawan hatsarin mota

car
Image caption Hatsarin mota

A Najeriya, hukumar kiyaye hadararruka ta kasa ta gudanar da wani babban taro a Jihar Kaduna, domin duba matsalolin da hukumar ke fuskanta wajen gabatar da aiyukanta.

Wannan ya kasance wani yunkuri ne na lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen rage yawaitar hadararruka a titunan Najeriya, wanda sau tari kan salwantar da rayukan al'umma.

Najeriya dai tayi kaurin suna a duniya a cikin jerin kasashe masu tasowa da ake samun yawaitar hadarurrukan mota.

Ana danganta wannan ne da batutuwa da suka shafi tukin ganganci, ko rashin kiyaye dokokin hanya, da tukin kananan yara da kuma rashin kyawun titina a ciki da wajen biranen kasar.