Jami'an Yemen sun kama wata da hannu a sakon bama bamai

Jami'an tsaro a Yemen sun bayyana cewa sun chafke wata mata bisa ga zargin tura sakonnin bama baman da aka gano a Birtaniya da Dubai.

Wannan dai ya biyo bayan wani aikin bincike da jami'an tsaron su ka yi, tun bayan gano sakonnin bama baman, wadanda aka nufi kai su Jihar Chicago a Amurla.

Da farko, Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun yi wa wani gida da matar da ake zargi ke boye, kawanya,.

Daga baya kuma jami'an tsaro suka bayyana cewa sun ma kama matar a babban birnin Sanaa.

Ana alakanta cewa kungiyar Al Qaeda da ke Yemen ce ke da alhakin aika wadannan bama baman.

Tuni dai jami'an tsaron Amurka suka dukufa wajen ganawa da takwarorinsu da ke yaki da ta'addanci a Yemen, wanda rahotanni ke bayyana cewa ana samun gagarumar nasara a binciken da ake yi.