Dan kunar bakin wake ya tashi bom a birnin Santanmbul

Wani dan kunar bakin wake ya tashi bom a tsakiyar birnin Santanbul na Turkiyya inda mutane sama da ashirin suka jikkata.

'Yan sanda sun ce sun gano gawar dan kunar bakin waken a dandalin Taksim, kusa da filin tunawa da samun 'yancin kasar.

Firaministan Turkiyya , Recep Tayyib Erdogan yace zasu saka kafar wando daya da duk wanda yake kokarin kawo rikici a kasar ko yin baraza ga zaman lafiyar kasar.