Rousseff ta lashe zaben Brazil

Dilma
Image caption Dilma ita ce mace ta farko da za ta shugabanci kasar

An zabi Dilma Rousseff a matsayin shugabar kasar Brazil, bayanda jami'an zabe suka ce ita ce ta lashe zagaye na biyu na zaben kasar da aka gudanar.

Ms Rousseff, 'yar shekaru 62, wacce wannan ne karo na farko da aka taba zabarta a kan wani mukami, ta zamo mace ta farko da za ta mulki kasar.

Ta yi alkawarin "girmama" kwarin guiwar da 'yan Brazil suka nuna a kanta, tare da yin aiki tukuru domin kawar da talauci.

Shugaba Lula ne ya zabe ta domin ta kasance magajiyarsa, bayan ya shafe zango biyu yana mulkin kasar, inda ya samu farin jini sosai.

Dubban magoya bayan jam'iyyar Workers' Party ne suka fita kan tituna domin murnar nasarar da ta samu.

Babbar kotun kula da zaben ta ce, bayan da aka kusa kammala kirga kuri'un baki daya, Ms Rousseff ta lashe kashi 56 cikin dari, yayinda abokin hamayyarta Jose Serra na jam'iyyar Social Democratic Party ya samu kashi 44.

Duk da cewa yin zabe wajibi ne a Brazil, an samu rahotannin jama'ar da ba su kada kuri'a ba da dama, wadanda yawan su ya kai kashi 21 cikin dari.