A Najeriya INEC za ta fara horo akan rejista

Image caption Shugaban hukumar INEC

A Nigeria a yau ne za'a soma wani horo na musamman ga wasu manyan jamai'an hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.

Horon wanda zai dauki kwanaki biyar ana bayarwa, zai kasance akan yadda za'a sarrafa na'urar da za'a yi amfani da ita wajen rajistar masu zabe da za'a yi nan gaba.

Ana saka ran cewa jami'an da za'a fara horarwa a yau din, sune kuma zasu horar da sauran jamai'an da zasu yi aikin rajistar.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da hukumar INEC din ke cigaba shan suka daga wasu da dama a kasar, wadanda ke cewa, hukumar tana tafiyar hawaiyi wajen tsara zabukan da za'a yi a badi.