Wani tsohon dan al-Qaeda ya tona mata asiri

Ibrahim Hassan
Image caption Ibrahim Hassan mutumin da ake zargi da aika bama-baman

Jami'an Burtaniya sun ce wani tsohon dan kungiyar al-Qaeda ne ya taimaka da bayanan da suka kai ga gano bama-baman da aka kama a Burtaniya da Dubai.

Jaber al-Faifi ya mika kansa ga mahukuntan Saudi Arabiya makwanni biyu da suka wuce, kamar yadda jami'ai suka shada wa BBC.

Jami'an Amurka sun ce wani dan kasar Saudiyya ne mutumin da suke zargi da kokarin aika bama-baman daga Yemen zuwa Amurka.

Daya daga cikin bama-baman an aika shi ne ta wani jirgin fasinja kafin a kama shi a Dubai.

An ce Jaber al-Faifi tsohon fursuna ne a sansanin Amurka da ke Guantanamo Bay, a kasar Cuba.

Bayan ya bar Guantanamo, ya samu horon tarbiyya a Saudiyya sannan ya sake shiga al-Qaeda a Yemen, kafin ya mika kansa ga jami'an Saudiyya. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito. Ya tuntubi jami'an Saudiyya inda ya bayyana musu cewa yana son komawa gida, abinda yasa aka shirya hakan ta hannun jami'an gwamantin Yemen, a cewar Mansour al-Turki mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ta Yemen.

Jaber al-Faifi na daya daga cikin fursunoni da dama da aka maida Saudiyya daga Guantanamo domin samun horo na musamman a watan Disamban 2006.