Mai yiwuwa makaman da aka kama a Najeriya daga Iran suke

Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad
Image caption Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad

Hukumomin Najeriya sun ce, akwai alamun da ke nuna cewa, makaman da aka kama a tashar jiragen ruwan Legas a makon jiya, daga Iran su ke.

Sai dai hukumomin sun ce har yanzu suna gudanar da bincike don gano wadanda suka dauki nauyin shiga da makaman kasar, da kuma inda aka yi nufin tura su.

Hukumomin na Najeriya sun kuma bayyana cewa, sun bukaci ofishin jakadancin Iran a kasar ya mika musu wani mutum da ake zargi da hannu a al'amarin.

Ofishin jakadancin na Iran dai ya yi kashedin cewa, yawan kalamai a kan batun ka iya jawo rudani.

A cewar minista a ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar, Dakta Aliyu Idi Hong, ko da yake ba a iya cewa kai tsaye makaman daga Iran suka fito, binciken farko-farko da hukumomin tsaron kasar suka gudanar ya nuna cewa, daga Iran din su ke, kuma akwai wasu Iraniyawan da aka gano cewa suna da hannu a shigowa da kwantenonin makaman.

Rahotanni dai sun bayyana cewa ya zuwa yanzu jami'an tsaron Najeriya na rike da wani dan kasar, wanda ake zargin yana da alaka da shigo da makaman, yayin da wasu Iraniyawa biyu kuma suka nemi mafaka a ofishin jakadancin Iran a Najeriya.

Dakta Aliyu Idi Hong ya ce don haka ne hukumomin Najeriya suka gayyaci jakadan Iran a kasar don ya yi musu bayani dangane da wannan al'amari, ya kuma mika musu wadanda ake zargin don yi musu tamabayoyi.

Ya zuwa yanzu ofishin jakadancin na Iran dai bai yi cikakken bayani a kan wannan al'amari ba.

Amma ya fitar da wata takarda wadda a ciki ya yi gargadin cewa, yin kalamai barkatai zai kara janyo rudu, don haka ya fi kyau a bari gwamnati ta gama bincike.