Amurka na farautar Ibrahim Al-Asiri

 Ibrahim Hassan Al-Asiri
Image caption Mutumin da ake zargi da hada bama-baman da aka aika da su Amurka

A kasar Yemen, an fara farautar Ibrahim Hassan Al-Asiri, wani mayakin kungiyar al-Qaeda, wanda ake zargi da dasa wasu bama bamai da aka gano a Burtaniya da Dubai ranar Juma'a.

Ibrahim Hassan al-Asiri, na daya daga cikin masu fafutukar da kasar Saudiyya ke nema ruwa a jallo.

An haife shi ne a kasar ta Saudiyya kimanin shekaru 28 da suka wuce, amma yanzu yana boye a kasar Yemen.

Yana da alaka da malamin nan haifaffen Amurka Anwar al-Awlaki, wanda tsohon abokin zaman fursunan sa ne a sansanin Gontanamo.

Har ila yau yana cikin shugabannin al-Qaeda a yankin kasashen Larabawa, kuma ana yi masa kallon mutumin da ya kware sosai wajen hada bom. Haka kuma ana yi masa kallon mutumin da ya hada bom din da kaninsa yayi amfani da shi wajen yunkurin kashe shugaban hukumar yaki da ta'addanci na kasar Saudiyya a watan Agustan bara.

Shugaban hukumar ya sha da kyar inda ya samu rauni, bayan da maharin ya tada bom din lokacin da yake wata ganawa da shi.

Har ila yau ana zargin Ibrahim Asiri, da shirya yunkurin tada bom a wani jirgin fasinjan Amurka a ranar Kirsimetin bara.

An yi amannar shi ne ya hada bom din da ake zargin Najeriya Faruk Mutallab ya boye a wondonsa domin tarwatsa jirgin.

Masu bincike na kwakwaf sun ce hanyoyin da yake bi wajen hada bom, na bayyana kwarewarsa da kuma horon da yake da shi, duk da cewa yawancin ayyukan na sa basu yi nasara ba.