Bom ya fashe a ofishin jakadancin Rasha a Girka

Harin a ofishin jakadancin Switzerland a Girka
Image caption Masu bincike na barin ofishin jakadancin Switzerland a Girka

Wani karamin bom ya fashe a ofishin jakadancin Rasha da ke Athens babban birnin kasar Girka.

'Yan sanda sun ce bam din ya tashi kafin isar kwararru kan kwance bama-bamai ofishin.

Fashewar ban din ta zo sa'o'i bayan fashewar wani abu da ake zaton bom ne a ofishin jakadancin kasar Switzerland a kasar ta Girka.

Babu dai wanda ya ji rauni a wajen. 'Yan sanda sun gudanar da bincike kan wasu sakwanni da ake zargi wadanda aka aike ofisoshin jakadancin wasu kasashe kwanaki biyun da suka wuce.

Ana dora alhakin kai jerin hare hare kan gwamnatin Girka da jami'an 'yan sanda a 'yan watannin nan kan masu tsattsauran ra'ayin sauyi.

Karamar na'ura ce aka jefa

Da farko dai ana ganin kamar wani sako ne dake kunshe da bom kwatankwacin wanda aka aike da shi zuwa ofishin jakadanci Mexico da ya tashi ranar Litinin a ofishin kamfanin aikewa da sakwannin.

Daga bisani jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa karamar na'ura ce da aka jefa cikin harabar ofishin jakadancin.

Kwararrun 'yan sanda kan har hada bama-bamai sun yi nasarar warware wasu kunshin sakonni bama bamai biyu wadanda aka aike zuwa ga ofishin jakadancin Bulgariya da kuma ofishin jakadancin kasar Chile.

Sai dai kamfanin da ke kai sakon da aka aike zuwa ga ofishin jakadancin kasar Chile ya firgita inda ya mika kunshin sakon ga jami'an tsaro wadanda suka warware bomb din dake cikin kunshin.