Rabuwar kawuna a kungiyar gwamnonin Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption A shekara mai zuwa ne za a gudanar zaben kasa a Najeriya

A Najeria, rahotanni na nuna cewa ana samun rarrabuwar kawuna a Kungiyar gwamnonin kasar game da zaben sabon shugaban kungiyar.

Takaddama dai ta kunno kai ne bayan kafafen yada labarai sun rawaito wasu daga cikin gwamnonin Nijeriya suna nesanta kansu daga zaben da wasu gwamnonin su ka yiwa gwamnan jihar Ogun, Mr Gbenga Daniel shugaban kungiya.

Abinda ke nuna cewa shi zai zamo magajin gwamna Bukola Sarki wanda ke shugabantar kungiyar.

Biyo bayan wannan takaddama, masana sun fara tofa albarkacin bakinsu kan ma'anar wannan rarrabuwar kai ga zabuka masu zuwa.

Ana sa ran kungiyar gwamnonin za ta yi wani taron gaggawa a ranar Laraba domin duba lamarin.

Da yake hira da BBC, Dr Abubakar Saddiq na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya danganta abin da yunkurin neman wanda zai tsayawa jam'iyyar PDP takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Ana yiwa kungiyar gwamnonin kallon mai karfin fada aji a fagen siyasar kasar musamman ma a jam'iyyar PDP mai mulki.