Nijar za ta jagoranci bunkasa kiwo a Afrika ta Yamma

Wasu makiyaya Abzinawa a Nijar
Image caption Wasu makiyaya Abzinawa a Nijar

A Jamhuriyar Nijar ma yau ne aka kammala wani taro da ya hada kwararru da masana a fannin noma da kiwo da suka fito daga kasashe mambobin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO.

Mahalarta taron sun tattauna ne kan yadda zaa bunkasa da inganta albarkatun noma da kiwo a yankin Afrika ta yamma.

Taron ya fi maida hankali ne a kan kan yadda za a samar da abinci da irin dabbobi ingantacce da ake iya yadawa a kasashen Afrika ta yamma.

An dai shirya taron ne tare da hadin gwiwar bankin duniya.